<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Zamanin dā, Almasihu Ɗan Allah
 Ya ji tausayinmu, mu ƃatattu.
 Shi ma ya rabu da gidan Ubansa
 Ya shigo duniyan nan tare da mu.

[V2]
 KORUS
 Zuwan Mai Ceto ƙauna ta sa shi,
 Allah ya bayar don duniya duk,
 Kada su ƃata, sai dai su sami
 Ceto da rai kuwa na har abada.

[V3]
 2) Zaman Mai Ceto a wurin mutane
 Da yawan so da alheri ya ke.
 Kowa ya nema ya gamu da Yesu.
 Ya dai same shi mai taimako ne.
 Korus

[V4]
 3) Zaman nan nasa na aikin alheri,
 Ba shi da aibi, mai ƙauna ne shi.
 Ransa ya bayar don fansar mutane,
 Allah ya karƃa, mai tsarki ne shi.
 Korus

[V5]
 4) Domin zunubinmu Yesu ya mutu,
 Bayan ya mutu ma sai binnewa.
 Shi ma ya tashi a rana ta uku
 Kāna ya hau Sama wurin Uba.
 Korus

[V6]
 5) Yesu Mai Cetonmu zai sake zuwa,
 Haka alkawari wanda ya yi.
 Sa zuciyarmu dai kowace rana,
 Bari ya iske mun shirya sosai.
 Korus</lyrics>
<title>Zamanin Dā, Almasihu Ɗan Allah LW140</title>
<hymn_number>140</hymn_number>
</song>